Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyayen Maharin London, Michael Adebolajo, 'Yan Nijeriya Ne


Ana ta aje sakonnin jaje daura da inda aka kashe sojan Burtaniya
Ana ta aje sakonnin jaje daura da inda aka kashe sojan Burtaniya

Yanzu an tabbatar cewa iyayen Michael Adebolajo, daya daga cikin mutane biyun nan da su ka kashe wani sojan Burtaniya a birnin London, 'yan Nijeriya ne.

Wakilin Muryar Amurka a London, Mohammed Sani Dauda, ya ce yanzu ta tabbata cewa iyayen Michael Adebolajo, daya daga cikin mutane biyun nan da su ka kashe wani sojan Burtaniya a birnin London, 'yan Nijeriya ne.

Sani ya ce tuni mutane su ka fara mayar da martani. Ya ruwaito wata musulma mai suna Lucky Awale na cewa, “a matsayimmu na musulmi a yanzu muna zama cikin halin dar-dar da rashin tabbas ne. ala tilas yau sai da na raka dana zuwa makaranta domin ina tsoron ko al'umma za su yi fushi da musulmi suyi mana wani abu.” lucky Awale ta kara da cewa, “koda kuwa wadannan mutane suna da sunan musulmi ne, wannan mummunan aiki ba hanyar musulmi ba ce.”

Yan siyasa kuwa, a lokaci guda sun yi baki daya ta yin tur da wannan mummunar katobara da su ka ce ta rashin imani ce, tare da kokarin kwantar da hankulan jama'a; da nufin kare aukuwar sabani a tsakanin al'ummar Kasa.

Wakilin na Muryar Amurka a birnin London ya kuma ruwaito Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron na cewa, “wadanda suka aiwatar da wannan tabargaza burinsu shi ne su rarrabamu; to amma lallai ne su san cewa irin wannan mummunan hali zai ma kara hada kan mu ne, ya kuma kara karfafa mana hali". Firayim Minista Cameron ya kuma mika jaje ga iyalin sojan da mutanen suka kashe, wanda hukumomi suka ce sunansa Drummond Lee-Rigby, dake bataliyar bindigogin Batare na Sojan Britaniya.

“Iyalinsa sun yi hasarar masoyi; mu kuma munyi hasarar soja jarumin maza", inji Mr. Cameron.

Sani ya saka muryar daya daga cikin maharani biyu mai suna Michael Adebolajo na cewa, "Da sunan Allah mu ba zamu kauce daga yakarku ba har sai kun daina yi mana shiga sharo ba shanu". Wasu daga kalamomin da suka fito daga bakin Michael Adebolajo kenan dan shekara 28, daya daga cikin samari biyu da suka yiwa sojan Burtaniyan yankan rago cikin bainar jama'a a kan titin unguwar Woolwich dake yankin kudu maso gabashin London.

To shi dai Michael Adebolajo haifaffen kasar Britaniya ne kuma ya girma ne a gundumar gabashin birnin London. An ce mahaifansa sun yi asali ne daga Nijeriya, kuma iyayensa kirista ne. Kamar shekaru goma da suka shige ne Michael Adebolajo ya shiga addinin Islama.

Anjem Choudry, wani limami a wata kungiya da aka haramta ta anan Britaniya da ake kira da Almujajiruun, kokuma mayaka, ya ce, “lokacin da yake halartar taron kungiyarmu, bai nuna wata alamar da ta bambantashi da kowa ba, kuma mutum ne mai biyayya. Ya kara da cewa kamar shekaru biyu kenan ban ji shi ba, sai kawai a cikin akwatin talabijin.

Wakilin na Muryar Amurka a London ya ce dangane da daya saurayin kuma har yanzu babu wani batu game da rayuwarsa. 'Yansandan yaki da tarzoma da 'yansandan ciki a yanzu duk suna gudanar da nasu binciken musamman kan cewa ma'aikatan tsaron kasa suna sane da su wadannan samari a matsayin masu tsattsauran ra'ayin Islama. A inda wannan al'amari ya faru kuwa har yanzu 'yansanda ciki na ci gaba da gudanar da bincike.

Sani ya ruwaito Mataimakin Kwamishinan 'yansanda, Simon Byrne, na cewa, “zamu bi diddigin komai da komai sai mun tantance musabbabin wannan al'amari da kuma yadda ma'aikatan tsaron suka tunkare shi".
XS
SM
MD
LG