Matashin nan shugaban kamfanin fitaccen shafin abotar nan Facebook wato Mark Zuckerberg (Zukabag) tare da matarsa Priscilla Chan sun gabatar da ‘yar su da suka haifa ga duniya tare da sadaukar da Dala Biliyan 45 da nufin tallafawa rayuwar jama’a a fadin duniya na zamanin nan da aka haifi ‘yar tasu da masu biyo bayanta.
A wata wasika da suka gabatar Mark da Chan sun yi alkawarin sadaukar da kashi 99 daga cikin dari na dukiyar da suka mallaka daga kason sun a kamfanin Facebook tsawon rayuwarsu.
Sun ce za su dauki lokacinsu wajen kasafta gudunmawar da suka dauki alkawarin sadaukarwa duniya. Kamfanin ya rubutawa hukumar saye da sayar da hannayen jarin Amurka cewa zasu dinga sayarwa ko sadaukar kason da ya kama daga cikin jarin sama da Biliyan daya kowace shekara har na tsawon shekaru 3 don ida nufin nasu.
An dai kafa Facebook ne a shekarar 2004 wanda ko a bara an ruwaito cewa ya yi nasarar tara kudin shigar da ya kai Dala Biliyan hudu da rabi. Kamfanin yace yana da masu shafuka akan shafin nasu sama da mutane Biliyan Daya a duniya. Sannan kaso 80 daga ciki suna wajen Amurka da kasar Canada ne, wato suna cikin fadin kasashen duniya ne.