A cikin irin bincike da ake gudanarwa a kasar Egypt, na binciko dukiya da abubuwan tarihi a karkashin kasa, an sake samo wani mutun-mutumin katako da aka sassaka na wata mata. Masanan dai sun bayyanar da wannan gunkin a matsayin matar sarki Pharaoh Amenhotep lll, wanda yayi zamani daga shekarar alib dubu daya da dari uku da casa’in da daya 1391 zuwa alib dubu daya da dari uku da hamsin da uku 1353, kamin bayyanar annabi Isah (A.S).
An dai tsunto wannan gunkin ne a garin Luxor, dake da tarinhin mutanen da. A cewar Mr. Sultan Eid, darakta a ma’aikatar binciken arzikin kasa, yace wannan gungi da aka gano na rataye da filawa, da wasu abubuwan hannu masu kala-kala, haka da wata sarka, ya kara da cewar wannan gunki ya samu wajen ajiya mai kyau, domin kuwa baiyi komai ba, kuma an kiyasta shekarun wannan mutun-mutumin zai kai shekaru dubu biyu da dari bakwai 2,700.