An bayyana dalilin da yasa Ministan Matasa da wasani na Najeriya, Barriter Solomon Dalung, ke sa tufafin khaki da jan hula, mataimakiya ta masamman ga Ministan Nneka Ikem Anibeze, tace shi dan gwagwarmaya ne wanda kuma ya damu da talakawa. Shi yasa yake sanya wa kuma haka zai ci gaba.
A wani labara kuma Minista Solomon Dalung, ya jinjinawa ‘yan wasan flying Eagles, a bisa nasarar da suka yi na doke kasar Mali, 3 da 2.
Da yake yabawa ‘yan wasan ta wayar talho, Ministan ya kuma umarce su da kada suyi kasa a gwiwa, a faggen taka leda har sai sun cimma samun gurbin zuwa gasar Olympics.
Yana mai cewa babu wani wasan mai sauki amma ganin yadda suka jajirce suka rikewa ‘yan Mali wuya ya nuna cewa sun nuna kwanjinsu na ‘yan Najeriya.
Da yake mayarda martini Kocin na Flying Eagles Samson Siasia, ya godewa Ministan da cewa kiran na Ministan zai karawa ‘yan wasan kwarin gwiwa, ya kuma baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa ba zasu bada kunya ba.