A Jahar Maradin Jamhuriyar Nijer, Kungiyar UNFPA Lafiya matasa ta kaddamar da wani littafi wanda zai wayar da kan jama’a akan auren wuri da kuma dole, biyo bayan la’akari da masan suka yi akan auren wuri da auren dole na haifar da matsaloli da dama ga diya mata, ga rahoton mani chaibou daga maradi.
Malama Monic Prisca wakiliyar kingiyar a Nijer ta yi bayanin cewa kashi arba'in da uku na 'yan mata, akan yi masu aure ne daga shekaru ashirin zuwa ashirin da hudu ko kamin shekaru goma sha biyar, kuma kashi arba'in da biyar cikin dari na 'yan shekaru goma sha biyar duk sunyi ciki.
Ta kara da cewa kasar ta Nijer ta yi kaurin suna wurin aurar da yara mata da wuri, kuma hakan na haddasa cututtuka masu nasaba da cutar yoyon fitsari, ko kuma rasuwar uwa da danta wurin haihuwa.
A sassa daban daban na jahar maradi, 'yan mata hamsin da shidda ne suka sami wannan horo akan auren dole da kuma auren yarinta.
Saurari cikakken rahoton.