Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buratai Ya Sake Bada Umarnin A Kamo Shekau A Raye Ko A Mace- Mene ne Hikimar Haka?


Janar Buratai a Sambisa
Janar Buratai a Sambisa

Janar Burtai ya sake bada wannan umarnin alokacin da ya kai ziyara a dajin Sambisa.

Da yake tsokaci kan wannan umarnin, Air Commodore Babagamawa mai ritaya, yace babu mamaki akwai hikima wajen sake bada wannan umarnin, domin hakan yana iya zaburadda dakarun su kara himma wajen ganin sun kamo Abubakar Shekau.

Gamawa, ya yaba da irin nasarori da sojojin suke kara samu kan 'yan ta'addan, ya bayyana fatar ganin an kawo karshen wannan ta'addanci baki daya ta ko wani fannin kasar.

Gameda tukuicin Naira milyan uku da rundunar sojojin ta ayyana ga duk wanda ya taimaka da bayanai da zasu ki ga kama Abubakar Shekau, yace a ganinsa sun wadatar, kuma wannan somin tabi ne.

Air Commodore Gamawa ya yaba da yadda gwamnati take kula da lafiya da jin dadin dakarun kasar.

Ga karin bayanin hirar da muka yi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG