Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Hafizan al-Qur'ani ta Najeriya, Sheikh Musa Hassan, yana daya daga cikin wadanda a can baya suka yi adawa suka ki yarda da wannan allurar rigakafin, amma a yanzu yace ya gamsu dari bisa dari da wannan magani, kuma ya amince da cewa tilas ne a kawar da wannan cuta daga duniya baki daya, ba ma Najeriya kawai ba.
Shugabar Kungiyar Musulmi Mata ta Najeriya, maryam Idris Othman, ta ce yana da muhimmanci a wayar da kan mata domin shawo kan maza masu kin jinin wannan allurar rigakafin.
Ga cikakken rahoton da Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko daga Abuja kan wannan taron bita da irin bayanan da shaihunan malaman suka yi.