Masana sunce wannan shiri zai bada kyakkyawar dama na kawar da cutar, wadda ake fama da ita tun 1950, kuma tana gurguntar da mutane da yawa kowacce shekara, amma an kusan kauda ta, ta wurin allurar rigakafi mai inganci da kuma fadakar da jama’a da ake yi.
Ya zuwa 2013, rahotonni da kuma bayanai na nuni da cewa, an sami kananan yara 19 dauke da cutar a kasashe uku - Pakistan, Afghanistan da Nigeria – bayan Indiya tayi bukin cika shekaru biyu da kawar da cutar.