Kungiyar lafiya ta duniya ta bayyana haka ne a cikin wani rahoto na hadin guiwa tare da kungiyar kula da cutar suga ta duniya (IFD) da kuma kungiyar cutar suga ta Nigeriya (DAN).
Bisa ga rahoton hadin guiwa da kungiyoyin suka rubuta, Nigeriya na da mafi yawan masu mutuwa daga cutar.
A cikin jawabinsa a wani shirin yaki da cutar ciwon suga a Lagosn,shugaban makarantar lafiya ta Jihar Osun, Prof Olutayo Alebiosu ya cewa, kashi 60% na mutanen da suke mutuwa,suna mutuwa ne ta dalilin kamuwa da cututtukan da ba’a dauka daga wani kamar ciwon suga da ciwon zuciya.
Profesa Alebiosu ya kara da cewa, za a sami nasara wajen rage mace macen sakamakon kamuwa da cutar tawurin lura, da kuma kyakkyawar kulawa da fiye da mutane miliyan daya dake fama da ciwon suga, da kuma fiye da wadansu miliyan 3.85 da wannan sinadarin da ake bukata a cikin jihi ya gaza masu a Nigeria.
Kwararru sun shawarci masu ciwon suga su rika zuwa asibiti domin a rika duba lafiyarsu da kuma yi masu gwaji a kai-a-kai.