Shugabannin kwamitin kwamitin gwamnati ne da ya kunshi likitoci da masanan kimiya da ake kira “USPSTF” a takaice, wanda suka hada kai domin bada hanyoyin kariyar cututtuka da kuma yin gwaje-gwaje suka bada wannan shawarar.
Kwamitin USPSTF ya bayar da wannan shawarar ne a shekara ta 2005 tare da bukatar ganin ana gwada mutanen dake da hatsarin kamuwa da cutar.
Amma masana sun bada shawarar yin sauyin da zai karfafa yin gwajin a matsayin hanyar kariya dake karkashin wannan doka.
Dokar lafiya ta Shugaba Obama, ta bukaci masu gwajin su bi umurnin kwamitin. Yanzu dokar lafiya ta bada ikon yin gwaji ga kowanne mutum tsakanin shekara 15 zuwa 65, wadanda ke da hatsarin kamuwa da cutar.