Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manoman Amurka Na Fatan Duk Wanda Ya Ci Zabe Ya Tallafa Musu


Jeff O'Connor yana duba waken soya a gonarsa
Jeff O'Connor yana duba waken soya a gonarsa

Manoman kasar Amurka za na shirin tafiya rumfunan zabe a ranar 5 ga watan Nuwamba domin zaben wanda su ke fatar zai kawo karshen matsin tattalin arziki da ke ci musu tuwo a kwarya.

A kowacce rana aka wayi gari John Ackerman da ke garin Morton na cike da fatan alheri da kyakkyawan budi, duk da kalubale da rashin tabbas din da ya ke fuskanta a gonarsa da ke jihar Illinois.

"A Illinois, muna da fiye da ekar noman kabewa fiye da 25,000 a cikin shekaru da yawa a cewar Ackerman."

Illinois ita ce jihar da aka fi noman kabewa a Amurka, kuma kabewar ke samawa Ackerman kusan rabin kudin shiga da yake samu. Ya noma kabewa da sauron yado danginta a wannan shekarar duk da farin da aka fuskanta.

Amma yanayi ba shine babban rashin tabbas din da Ackerman ke fuskanta ba. Ya na kuma da damuwa game da rashin tallafin kudi daga wasu manyan dokokin tallafa wa manoma da ake kira farm bill da turanci, wanda ya ce "tallafin na ba shi damar sayen inshora."

Kananan manoma kamar Ackerman sun dogara ne ga tallafin na farm bill don taimaka musu biyan kudin inshorar amfanin gona, wadda ke taimaka musu samun kudi daga masu ba da rance don su ci gaba da aikin noma.

Girbin waken soya
Girbin waken soya

Ackerman ya ce "Idan ba zan iya nuna musu cewa zan iya sayen inshorar da zata kareni a lokacin da wani bala'i ya auku ba, hakan zai shafi damar samun rance."

Inshorar amfanin gona ita ke da kashi kusan 10 cikin 100 na fiye da dala tiriliyan 1 na tallafin da ake kira "dokar gona" a cikin shekaru 10.

A ranar 30 ga watan Satumba aka kawo karshen tallafin na "dokar gona" a daidai lokacin da ake tafka muhawara tsakanin ‘yan majalisa kan sabunta dokar. A yanzu Majalisa na hutu har zuwa lokacin zaben shugaban kasa da ke tafe, shi ma wani babban batu da ke kawo rashin tabbas ga Ackerman.

"Kudaden shiga da ake samu ta hanyar noma zasu ragu sosai a wannan shekarar, a cewarsa."

Ackerman ya danganta hakan da tsadar kayan aikin gona kamar taki da ake fuskanta, da kuma karancin farashin masarar da waken soya da ya noma. Ya ce farashin ya yi kasa ne saboda ta wani bangaren China ta sanya haraji kan waken soyar Amurka a matsayin maida martani kan harajin da gwamnatin Trump ta sanya kan karafunan China, matakan da aka ci gaba da amfani da su har a karkashin gwamnatin Shugaba Joe Biden.

"An samu raguwar kayan da China ke saye, a saboda haka manoma harajin zai fara shafa."

Zaman majalisar dokokin Amurka
Zaman majalisar dokokin Amurka

Muhawara game da karin kudin haraji a lokacin yakin neman zaben Shugaban kasa na Amurka na kawo damuwa ga Ackerman, da kuma David Iserman shi ma manomi mazaunin birnin Streator, a jihar Illinois, wanda ya ce "lamarin na ba shi tsoro."

Yayin da Isermann ke sarrafa amfanin gonarsa da aka girbe daga gonakinsa, yana ta waswasi kan ko ya sayar da hatsinsa yanzu, ko kuma ya adana, da fatan a sami karin farashi nan gaba. Amma ya damu da tasirin harajin nan da lokaci mai tsawo.

"Mun rasa gurbin gaba-gaba na hada-hadar kasuwancin waken suya da China, wacce ta koma harka da kasashen nahiyar Amurka ta kudu."

Gonar waken soya a Illinois
Gonar waken soya a Illinois

“Muna bukatar sabbin kasuwanni. Muna bukatar kasuwannin da zamu kai amfanin gonar mu.”

Ryan Whitehouse, shi ne darakta a fannin yin dokokin kasa a ofishin harkokin noma na jihar Illinois, wanda ke ba 'yan majalisa shawarwari game da manoma.

"Tabbatar da cewa ba a sanya haraji ba, shi ne babban abin da wannan kungiyar ta ba fifiko."

Isermann ya ce takaddamar kasuwancin da ake yi da China ba farashin amfanin gona kadai ya shafa ba.

"Takaddamar ta janyo karin farashin kayan aiki da yawa saboda an sami karin farashin karahuna da dalma kuma akwai karahuna da dalma da yawa a kayan aikin gona."

Gwamnatin Trump ta ba manoma karin tallafi don sassauta tasirin harajin da aka sanya, amma duk da haka matakin bai kawar da asarar da Isermann ya yi ba.

"Ba na tunanin tallafin ya taimaka mana akan duk asarar da muka yi, a cewar Isermann."

Ackermann na fatan duk wanda ya ci zaben shugaban kasa, da kuma kujerun majalisar wakilai da dattijai na Amurka a wannan shekarar, zasu tuna da manoma.

“Shin muna samun wakilcin da ya dace? A gaskiya Ba na tunanin haka, a cewar Ackerman.

Duka Isermann da Ackerman sun ce zartar da kudurin "dokar gona" ba tare da bata lokaci ba na da matukar muhimmanci, ko ma wacce jam’iyya ce ke jagorantar gwamnatin bayan ranar zabe.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG