Abuja, Najeriya. —
Shirin a wannan makon ya yada zango a babban tarayar Anjeriya Abuja, ina wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ta jagoranci tattaunawa da baki guda uku, da Muktari Dan Mallam da Danjuma Abdullahi da Fatima Dabo Kan zaben shugaban kasa a Amurka wanda za a yi ranar talata 5 ga watana Nuwamba shekara 2024.
Sun kuma tattauna akan yadda zaben ya dau hankali musamman kasancewar wannan shine karo na biyu da mace ta tsaya takaran kujerar shugaban Kasa a Amurka, sannan a lokacin gangamin yakin neman zaben su an lura cewa suna tafiya kusan Kunnen doki a maki da manazarta ke baiwa 'yan takaran. Ko wannan zai iya sauya wani abu a Kasara Amurka?
A saurari shirin tare da Madina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna