A yau Laraba, kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS) ta amince da ficewar 3 daga cikin tsaffin mambobinta Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar daga cikinta, al’amarin da ya fara aiki tun daga yau 29 ga watan Janairun da muke ciki, bayan cikar wa’adin shekara guda da aka gindaya.
Sai dai, saboda tabbatar da hadin kan kasashen yankin, ECOWAS ta umarci mambobinta da su ci gaba da amincewa da fasgo din tafiye-tafiyen kasashen 3 da ke dauke da alamar kungiyar har sai abin da hali ya yi.
A cikin wata sanarwa, hukumar ECOWAS ta kara da cewar kofofinta zasu cigaba da zama a bude domin karin tattaunawa da kasashen 3.
“Hukumar ta kafa wani tsarin da zai ba da damar tattaunawa game da wadannan tsare-tsare da kowace daga cikin kasashen 3. Wannan sako ya zama wajibi domin kaucewa rudani da katsewar rayuwa da harkokin al’ummominmu a wannan lokaci na sauyi,” kamar yadda sanarwar ta zayyana.
Kasashen 3 da ke karkashin mulkin soja sun sanarda ECOWAS a hukumance game da shirinsu na ficewa daga cikinta nan take a watan janairun 2024, inda suka kafa hujja da tsananin dogaron da kungiyar ke yi akan kasar Faransa.
Kasashen 3 na yankin sahel sun kafa ta su kungiyar mai suna “Kawancen Kasashen Sahel” (AES).
Dandalin Mu Tattauna