Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Yi Duk Mai Yiwuwa Don Hana Kasashen AES Ficewa Daga ECOWAS - Gwamnatin Najeriya


Nigerian Minister of Foreign Affairs, Yusuf Tugga
Nigerian Minister of Foreign Affairs, Yusuf Tugga

"Daga karshe za su yi nadama duk kasashen 3 ba su da iyaka da teku in za su shigo da kaya sai ta Benin, Senegal ko Najeriya.”

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi duk abun da ya dace tayi don ta dakatar da Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso daga ficewa daga kungiyar ECOWAS amma duk yunkurin ta ya ci tura.

Bayanan na gwamnatin Najeriya ta bakin ministan harkokin wajen kasar Yusuf Tugga, na zuwa ne a karshen wa’'adin ficewar kasashen a watan nan na Janairu duk da cewa ECOWAS ta kara musu wa’adi wata 6.

Kazalika, kasashen uku sun kaddamar da matakin buga sabon fasfo don jingine amfani da na ECOWAS da yake ba ‘yan kasashen kungiyar damar zirga-zirga ba shamaki.

Wakilin Muryar Amurka a Abuja, babban birnin Najeriya, Nasiru Adamu El-Hikaya, ya ruwaito cewa, Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tugga, ya ce sun dau duk matakan ‘yan uwantaka da diflomasiyya don jan hankalin kasashen su zauna da dangi amma ba sakamako mai karfafa guiwa, “ba irin kokarin da ba a yi. Ni din nan na yi yunkuri ba sau daya ba sau biyu ba, in tashi in je ko kuma mu ce mun gaiyace su, su ki zuwa.” Inji Yususf Tugga.

Duk da su na karkashin mulkin soja, Yusuf Tugga ya ce an yi wa kasashen tayin kudin tallafin tsaro da kayan aiki don a nuna musu cewa ana tare da su, duk da tankiyar da ke tsakanin su da uwar kungiya ECOWAS.

Ga kalaman zargin Nijar kan Najeriya da ta ce tana hada kai da Faransa don birkita Nijar, Tugga ya ce zargin ya ba gwamnatin Najeriya mamaki kuma bahi da tushe balle makama.

Nasiru ya ruwaito cewa, tsohon jakadan Najeriya a Afurka ta kudu Sulaiman Dahiru, ya ce ba farar dabara ba ce kasashen uku su dau zabin ficewa daga ECOWAS don hakan zai kawo illa ga tattalin arzikin su; “ba ruwan su da ECOWAS amma na sha fada daga karshe za su yi nadama duk kasashen 3 ba su da iyaka da teku in za su shigo da kaya sai ta Benin, Senegal ko Najeriya.”

A latsa nan don a saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:

NIGERIA ECOWAS POISED TO STOP NIGER OTHERS FROM EXIT.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG