Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Soumaila Cisse Ya Gana Da Shugaban Rikon Mali Bayan Sako Shi


Magoya bayan Soumaila Cisse da aka sako
Magoya bayan Soumaila Cisse da aka sako

Tsohon dan takarar shugaban kasar Mali Soumaila Cisse ya gana da shugaban rikon kwaryar kasar a daren ranar Alhamis 8 ga watan Oktoba karon farko tun bayan sakinsa a wannan makon da masu kaifin kishin Islama suka yi a wata musayar fursunoni.

Cisse, wanda aka sace watanni shida da suka gabata, bai bayyana yanayin tattaunawar da ya yi da Bah N’Daw da sauran manyan mutane a fadar shugaban kasar da ke Bamako babban birnin kasar ba.

Cisse ya yi magana ne kawai game da garkuwar da aka yi da shi, yana mai cewa galibi ya kasance cikin kadaici yana rayuwa a cikin mawuyacin yanayi, amma ba a azabtar da shi ba.

Masu tsattsauran ra'ayin addini sun saki Cisse da wasu Turawa uku a arewacin Mali, kwanaki kadan bayan da gwamnatin ta Mali ta saki kusan mayaka 200, duk da cewa ana nuna damuwa sakin nasu na iya kara dagula kasar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG