Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gamayyar Kungiyoyin Malaman Makaranta A Nijar Na Yajin Aiki


Hadakar kungiyoyin malaman makaranta kimanin sittin da ake kira “CAUSE” da hadin guiwar kungiyar malman makaranta ‘yan kwantaregi sun gudanar da taron gangami don sake salon tafiya game da tauye musu hakki da suka ce gwamnati nayi.

Wani dan kungiyar ta “CAUSE” Gali Dauda, ya ce matsalolin sun hada da na albashi da kuma bukatar cewa malamai su ci gaba da koyar da dalibai al halin suna bin bashin albashi.

Yana mai cewa a kowane lokaci sai a dingi batun cewa babu kudi amma manyan kasa na yin abinda suke so, ya kara da cewa idan har ana bukatar a rage kudaden ma’aikata ne toh ya kyautu a fara daga shugaban kasa kafin ya zo kan kananan ma’aikata, koda yake a cewar Malam Gali, an fara tattaunawa tsakanin kungiyarsu da Gwamnati.

Babban darakta na hukumar ilimi na jihar Damagaram, Baru Shekarau, yace tuni aka fara biyan albashin, ya kuma hakkinsu ne su fadi abinda yake damuwarsu a dauka akai gaba domin magacewa amma su koma bakin aiki domin kada a cutar da yara.

Malaman jami’a, a jihar Damagaram, suma sun fara wani yajin aiki na kwanaki ukku, suma akan rashin biyansu albashi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

XS
SM
MD
LG