Sakataren Tsaron Amurka Ashton Carter ya fada ranar Talata cewa a karkashin sabon salon Amurka zai kunshi kara kai hare hare da jiragen yaki da kuma kai farmaki da sojojin-kasa.
Kakakin fadar white House Eric Shultz ya tabbatar da bayanin da sakataren tsaron na Amurka yayi cewa, "karara Amurka tana da karfin kai farmaki jifa-jifa a Syria tareda hadin gwuiwa da kawayenta dai dai da zarafi da ta samu domin yin haka."
Ahalinda ake ciki kuma uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama, zatayi balaguro zuwa Qatar da Jordan makon gobe idan Allah Ya kaimu, domin karfafa kamfen da take yi na ganin an saka mata makaranta.
Madam Obama zata yi jawabi ga a taron koli na shugabannin harkokin ilmi daga sassan duniya daban daban da za'a yi a Doha.Taron da ake yi shekara shekara yana nazarin hanyoyi sahihai na inganta neman ilmi a fadin duniya.
Daga bisani zata je Jordan zata ziyarci wata makaranta da aka gina tareda taimakon da Amurka ta bayar kuma ta gana da 'yan mata dalibai. Uwargidan shugaban na Amurka zata jinjinawa Jordan saboda abunda Fadar White House ta kira "karamcin kasar da dukufarta wajen ilmantar dukkan yara da suke cikin kasar,ciki harda yara daga Syria wadanda suka sami mafaka a kasar.
A yayin wannan ziyarar Mrs Obama zata kuma ziyarci mayakan saman Amurka wadanda suke wani sansani dake bayan garin Doha.