'Yan majalisun daga bisani sun nuna alhininsu kan matasan da suka rasa rayukansu babu gaira babu dalili. 'Yan majalisar sun musanta zargin da aka yi masu cewa an riga an raba masu guraben ayyukan kafin a sayarda takardun jarabawar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane goma sha tara. Takwas sun mutu a Abuja. An samu mutuwar mutane uku a Minna da biyar a Fatakwal da uku a Benin ta jihar Edo.
Daga bisani majalisar ta baiwa kwamitocin dake kula da ma'akatar shige da fice mako daya su gudanar da bincike kuma su kawo rahoto gaban majalisar.
Shugaban kungiyar kwadago na kasa Abdulwaheed Umar ya yi tur da yadda ma'aikatar shige da fice ta gudanar da jarabawar inda yace sun lura cewa da gangan aka shirya jarabawar ba domin komi ba domin dan abun da zasu samu. Sayarda takardar neman aikin kan nera dubu daya ga kowane mai neman aiki shi ya kara ma hukumar karfin gwiwar ta yi hakan, wato ba komi ba ne illa son kudi. Yace idan aka duba abun babu adalci. Umar yace tara mutane a filin kwallo a ce nan ne za'a yi masu jarabawa wulakanci ne ga jama'a. Yace kuma kowa ya san karya ne domin wadanda za'a dauka 'yan kadan ne. Yace sun yi allawadai da lamarin kuma dole a bincika kuma gwamnati ta dakatar da shirin.
A wata sanarwa dake dauke da sa hannun mai magana da yawun PDP Oliseh Metuh ya bayyana mutuwar matasan da cewa abun takaici ne. Ita ma jam'iyyar adawa tace gwamnatin tarayya ta yi gaggawan tsige ministan shige da fici Abba Morro a bisa laifin rashin iya aiki.
Ga karin rahoto.