Opishin jakadancin kasar Uruguay yace Amurka, Koriya ta Kudu (KTK) da Japan ne suka nemi a yi wannan taron.
Sai dai kuma yayinda ake shirin taron, ita kuma KTA ta bada sanarwar cewa ta kamalla shirin kera karin makamai masu linzame masu cin matsakaicin zango da kuma harba su.
Gwamnatin KTK tace rokan da KTA ta harba jiya Lahadi, an harba shi ne daga wani wuri dake cikin lardin Pyeongan na kudancin kasar, kuma yayi tafiyar km 500 kafin ya fado cikin Tekun Japan.
Wannan shine gwajin harba makamai na biyu da KTA tayi a cikin mako guda, kuma shine na 10 a cikin wannan shekarar
Facebook Forum