Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Donald Trump Ya Caccaki Iran Yayainda da Sauka Israila


Shugaban Amurka Donald Trump da Firayim Ministan Israila Bejamen Netanyahu
Shugaban Amurka Donald Trump da Firayim Ministan Israila Bejamen Netanyahu

Shugaba Donald Trump na Amurka ya caccaki take-taken tsokana da manufofin kasar Iran a lokacinda ya sauka a Isra’ila a yau Litinin don kai ziyararsa ta farko a kasar ta Yahudawa tun bayanda ya zama shugaban Amurka.

Trump yace a lokaci yayi da ya kamata Amurka da Isra’ila su hada karfi, su yaki abokan adawansu kamar kungiyar ISIS da kasashe irinsu Iran masu bada goyon baya ga kungiyoyin ‘yan ta’adda masu tada fitinnu a a cikin duniya.

Shugaba Trump dai yana wannan jawabin ne a birnin Kudus yayinda yake tsaye tareda shugaban Isra’ila Reuven Rivlin, ana sa’oi kadan kafin tarukkan da zaiyi da pr-ministan kasar Benjamin Netanyahu da kuma kai ziyara zuwa wajen wasu muhimman wurare masu muhimmanci na mabiya addinin Yahudanci da Kiristanci.

Trump dai ya shiga Isra’ila ne daga Saudi Arabia inda yace sarkin kasar Salman ya tabattar mishi da cewa suna son ganin an shata sulhu tsakanin Yahudawa da Palesdinawa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG