Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Ne Tsakanin Miyagun Mutanen Dana Kirki: In Ji Trump


Dopnald Trump baiyi anfani da kalimar “akidar Islam ta matsanancin ra’ayi”, kamar yadda ya saba yi baya lokacinda yake yakin neman zabe.

A cikin wani muhimmin jawabin da ya gabatar yau a Saudi Arabia, shugaban Amurka Donald Trump yayi kira akan kasashen Musulmi da su hada kai da Amurka wajen yakar akidar ta’addanci da matsanantan ra’ayoyi.

A wannan jawabin da yake a tafiyarshi kasashen ketare ta farko tun bayanda aka zabe shi, Trump yace yana son ganin an hada hancin kasashen da ke da manufa irin daya, ta ganin bayar akidar ta’addanci, abinda yace “yaki ne tsakanin mutanen kirki da miyagun mutane.”

Yace ba wai munzo ne a nan don yi wa duniya lacca ba. Ba muzo nan don gayawa . kowa cewa ga abinda zaiyi ba.

Haka kuma shugaban ya nuna yadda akasarin wadanda ke rasa rayukkansu ko jikkata a hare-haren ta’addanci, 90% nasu, duk Musulmi ne kansu.

Shugaban na Amurka yace “wannan ba yaki bane tsakanin addinai, dariku ko wasu karnoni, wannan yaki ne a tsaakanin wasu mutane dake son ganin bayan duk bil adaman dake bisa doron duniya” da kuma mutanen arziki mabiya dukkan addinai dake son kare duniyar tamu.”

Sai dai a wannan jawabin nashi, Trump, wanda ke son hana wa mutanen kasashen Musulmi shidda shiga Amurka, baiyi anfani da kalimar “akidar Islam ta matsanancin ra’ayi”, kamar yadda ya saba yi a can baya lokacinda yake yakin neman zabe.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG