Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban TikTok Zai Ba Da Bahasi A Gaban Majalisar Dokokin Amurka Game Da Lamarin Tsaro


TECH-TIKTOK/
TECH-TIKTOK/

Shugaban TikTok Shou Zi Chew zai bayyana a gaban Kwamitin Makamashi da Kasuwanci na Amurka a watan Maris, yayin da 'yan majalisa zata tantance manhajar bidiyon mallakar kasar China.

Shugaban TikTok Shou Zi Chew zai bayyana a gaban Kwamitin Makamashi da Kasuwanci na Amurka a watan Maris, yayin da 'yan majalisa za su tantance manhajar bidiyon mallakar kasar China.

Chew zai ba da bahasi a gaban kwamitin a ranar 23 ga Maris, wanda zai kasance karo na farko a gaban kwamitin majalisar, in ji ‘yar majalisa wakilai ta jami’iyyar Republican kuma shugabar kwamitin Cathy McMorris Rodgers, a wata sanarwa a ranar Litinin.

Labarin na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin kula da harkokin kasashen waje na majalisar wakilai ke shirin kada kuri'a a wata mai zuwa kan kudirin dokar hana amfani da TikTok a Amurka saboda matsalolin tsaron kasa.

"TikTok mallakar ByteDance yana sane ya ba da dama ga jam'iyyar Kwaminisanci ta China ta sami damar shiga bayanan Amurkawa masu amfani da manhajar," in ji McMorris Rodgers, ta kuma kara da cewa Amurkawa sun cancanci sanin yadda wadannan ayyukan ke shafar sirrinsu da bayanansu.

TikTok ya tabbatar a ranar Litinin Chew zai ba da bahasi.

McMorris Rodgers da sauran 'yan majalisar Republican sun bukaci karin bayani daga TikTok. Suna son sanin tasirinsa ga matasa yayin da ake fama da damuwa game da abubuwa masu cutarwa na TikTok, kana sun nemi karin cikakkun bayanai kan yiwuwar lalata kananan yara a dandalin, in ji sanarwar.

A cikin shekaru uku da kasancewar TikTok - wanda Amurkawa sama da miliyan 100 ke amfani da shi – an nemi ya tabbatar wa da Washington cewa ba za a iya samun bayanan sirri na Amurkawa ba kuma jami’iyyar Kwaminisanci ta China ko wani da Beijing keda iko a kan shi ba zai iya shiga cikin kundin TikTok ba.

Kwamitin gwamnatin Amurka kan zuba jari na kasashen waje a Amurka (CFIUS), wata kungiya mai karfi ta tsaron kasa, a cikin 2020 ta umarci ByteDance da ta karkatar da TikTok saboda fargabar cewa za a iya mika bayanan Amurkawa masu amfani da manhajar ga gwamnatin China.

CFIUS da TikTok sun shafe fiye da shekaru biyu suna tattaunawa da nufin cimma yarjejeniyar tsaron kasa don kare bayanan masu amfani da TikTok na Amurka.

Majalisar dokokin Amurka za ta kada kuri'a a wata mai zuwa kan yiwuwar haramta TikTok.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG