A wasikar da Alhaji Lai Mohammed wanda yake magana da yawun jam'iyyar ya aikawa Muryar Amurka ya ce ba komi ba ne illa kokarin hallaka 'yan jam'iyyar ta yin anfani da jirgin sama. Ya ce akwai bukatar a gaggauta binciken lamarin domin gujewa jefa rayuwar jama'a cikin hadari. Hana jirgin sauka ya fi ma yunkurin da aka ce gwamnati na yi wajen hallaka wasu kamar yadda wasikar Obasanjo ta ambata. Ya ce bai dace a ce komi ana sa siyasa cikinsa ba.
Mr. Yakubu Datti wani jami'in zirga-zirgar jiragen sama ya ce akwai ka'idodi da suke bi a harkar tashi da saukar jirgin sama. Ya ce korafin da APC ke yi babu gaskiya ciki. Filin jirgin saukan jirgin sama dake Gombe bai saba ganin jirage ba. Don haka ranar da suka dauki jirgi zuwa Gombe ana aiki a filin dalili ke nan aka rufeshi na wasu sa'o'i biyu da aka gama aikin aka bude. Datti ya ce babu gaskiya a korafin amma ya yi alkawarin zasu bincika ko matukin jirgin ya sanarda filin lokacin da zai tashi da lokacin da zai isa Gombe.
Datti ya ce maganar ta fito ne daga 'yansiyasa. Idan akwai abun damuwa daga wurin matukin jirgin ya kamata su ji. Wani direban jirgin sama Ado Sanusi ya ce idan jirgi zai tashi daga wani gari zuwa wani zai shirya tashinsa kana ya mika ga mahukunta. Idan an amince to ya san idan ya tashi daga wanan garin ana jiransa a wancan garin. Daga an saka wannan bayani cikin naura mai kwakwalwa inda zai sauka sun sani nan da nan. To saidai babu irin wannan tsarin a Najeriya.
Ga karin bayani.