Kudirin neman yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya garanbawul wajen kirkirar wa’adin shekaru 6 falan daya ga mukamin shugaban kasa da gwamnoni bai tsallake ba a majalisar wakilan kasar.
Kudirin da dan majalisa Ikenga Ugochinyere ya gabatar ya nemi a amince da raba Najeriya zuwa shiyoyi 6, da zasu rika yin karba-karba a kan mukamin shugaban kasa sannan gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi za su kasance a cikin hurumin wadannan shiyoyi.
Haka kudirin ya nemi a ba da damar gudanar da dukkanin zabubbukan kasar a rana guda.
Lokacin da aka kada kuri’a domin yin karatu na 2 a kan kudirin, galibin ‘yan majalisar sun ki amincewa da shi.
An taba yin fatali da makamancin kudirin a dai dai wannan gaba sa’ilin da dan majalisa John Dyegh ya gabatar da shi a 2019.
Dandalin Mu Tattauna