Majalisar Dattawan Najeriya ta amince Shugaban kasar, Bola Tinubu ya ranto naira tiriliyan 1.77 a matsayin sabon tsarin rancen aiwatar da dokar kasafin kudin bana daga ketare.
Majalisar Dattawan, karkashin jagorancin mataimakin shugabanta, Barau Jibrin, ta amince da bukatar karbo rancen ne bayan da kwamitinta akan rancen cikin gida dana ketare da Sanata Magatakarda Wammako ke jagoranta ya gabatar da rahotonsa.
Za a yi amfani da rancen wajen cike gibin Naira tiriliyan 9.7 dake cikin kasafin kudin na bana.
A ranar Talata Shugaba Tinubu ya aikewa Majalisar Dokokin kasar, da wasikar neman sahalewa ya ranto bashin Naira tiriliyan 1.77 a matsayin sabon tsarin rancen aiwatar da dokar kasafin kudin bana.
Haka kuma, Shugaba Tinubun ya aike da matsakaicin kasafin da za’a kashe tsakanin 2025 da 2027 ga majalisar tare da kudirin neman yin garambawul ga shirin tallafawa al’ummar kasar, da nufin mayar da kudin bayanan ‘yan kasa ya zama abinda gwamnatin tarayya za ta rika amfani da shi wajen aiwatar da shirye-shiryenta na ba da tallafi.
Hakan na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan babban bankin Najeriya ya bayyana cewar gwamnatin kasar ta kashe dala bilyan 3.58 wajen biyan basussukan da ake binta a ketare a watanni 9 na farkon shekarar 2024 da muke ciki.
Dandalin Mu Tattauna