Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Kudirin Neman Yin Zabe Daga Ketare Ya Tsallake Karatu Na 2   


Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)
Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)

Kudirin neman yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima da kuma samar da damar yin zabe daga wajen kasar ya tsallake karatu na 2 a Majalisar Wakilai a yau Laraba.

Kudirin, da hadakar Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, da dan amajalisa Sadeeq Abdullahi suka gabatar, na neman ayi gyara akan dokar zaben 2022 tare da samar da damammaki ga ‘yan Najeriyar dake zaune a wajen kasar suyi zabe.

A watan Yulin daya gabata ne aka zartar da kudirin domin karatu na 2, kuma tuni aka tura shi zuwa kwamitin kula da harkokin zabe domin ci gaba da mahawara a kansa.

Sai dai, bayan daya tsallake karatu na 2 a jiya Talata, an tura kudirin zuwa kwamitin gyaran kundin tsarin mulki domin ci gaba da mahawara a kansa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG