Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Kasafin Kudin Da Zai Hana Rufe Ma’aikatun Gwamnati A Amurka


Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, Mike Johnson
Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, Mike Johnson

Idan har Majalisar Dattawa ta ki amincewa da kudurin kasafin kudin, babu makawa sai an rufe wasu ma’aikatun gwamnatin kasar.

Majalisar Wakilan Amurka ta amince da kudurin kasafin kudin da gwamnati za ta kashe cikin watanni shida masu zuwa, lamarin da ya sa ake tunanin an dauki hanyar kaucewa rufe wasu ma’aikatun gwamnatin.

Yanzu kudurin kasafin kudin na Dala tiriliyan 1.2 zai nausa zuwa Majalisar Dattawa wacce ake kyautata zaton za ta amince da shi nan da daren Juma’a zuwa ranar Asabar.

Kudaden da gwamnatin ke kashewa za su kare da karfe 12:01 na safiyar Asabar, kodayake, ba lallai ba ne Amurkawa su ji radadin rufe ma’aikatun gwamnatin idan lamarin ya fado a karshen mako.

Idan har majalisar dattawa ba ta amince da kudurin ba, babu makawa sai an rufe wasu ma’aikatun gwmnati.

‘Yan jam’iyyar Democrat da ke majalisar ta wakilai da dama ne suka goyi bayan kasafin a lokacin da aka kada kuri’ar da ta nuna mambobi 286 ne suka amince yayin da 134 suka nuna adawa da kasafin.

An jima ana dage kudurin kasafin kudin cikin ‘yan watannin da suka gabata inda akan amince da na wucin gadi domin ma’aikatun gwamnti su ci gaba da aiki.

Kikikakar da aka fuskanta a majalisun dokokin Amurka kan kudurin kasafin kudin, ta kara fito da rarrabuwar kawunan da ke tsakanin ‘yan Republican masu rinjaye a majalisar wakilai.

Kazalika lamarin ya kara fito da irin kalubalen da ake fuskanta a duk lokacin da aka ce an raba shugabancin majalisun dokokin kasar biyu tsakanin ‘yan Democrat da Republican.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG