Duk da cewa, sauran kasashen duniya basu ga watan azumi ba, a Jamhuriyar Nijar majalisar koli ta addinin Musulunci, ta tabbatar da ganin watan Ramadan, ke nan za’a tashi da azumi yau Laraba.
Daya daga cikin mambobin majalisar, da ya yi jawabi a madadin shugaban majalisar, Shaikh Muhammad Ag Ahmed Shafiu, yace “majalisar tana shaidawa hukumomin Nijar cewa an ga wata” cikin jihohi biyu, Dossou da Diffa. Yace yanzu ta tabbata ranar Laraba 16 a watan Mayu za’a fara azumi a kasar ta Nijar.
Shi ma Firayim Ministan Kasar Birji Raffini ya yi jawabi a madadin hukumomin kasar dangane da ganin watan na Ramadan. Y ace kamar yadda aka saba ya k an yi jawabi yayinda za’a kama azumi a kowace shekara a madadin shugaban kasa. Ya yiwa ‘yan kasar fatan alheri yayinda suke gudanar da ibadar.
Firayim Ministan ya tunawa al’ummar kasar cewa watan azumi wata ne mai albarka, watan da ake yiwa juna gafara tare da samun gafara, kuma shi ne shika shikai na uku a addinin Islama.
Haka ma wasu ‘yan kasar suka bayyana fatansu yayinda suke shirin soma azumin wannan shekarar. Sun yi fatan yadda aka ga watan lafiya, Allah ya sa, su yi azumin lafiya.
Ga rahoton Haruna Bako da karin bayani
Facebook Forum