Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makwaftan Libiya Sun Yi Taron Karfafa Tsaro


Africa's Sahel Region
Africa's Sahel Region

Kasashen Chadi, da Libya, da Nijar, da kuma Sudan na gudanar da taro a Birnin Yamai domin tattaunawa kan hanyoyin karfafa matakan tsaron iyakokin kasashen hudu.

Taron wanda na wuni daya tak ne na matsayar wata damar chanja yawu tsakanin ministocin dake kula da harkokin cikin gida da takwarorin su na tsaro da masu kula da harkokin waje ba'idin manyan hafsoshin soja da jami'an samar da bayanan sirri a wani yunkurin zakulo ingantattun hanyoyin warware matsalolin da ke da nasaba da rikicin kasar Libiya inji mininstan tsaron Nijer Alhaji kalla Muntari inda yace matsalar da ke cikin Libiya tafi karfin kasa guda kuma matsalar da take kawowa kasashen makwaftan ta yafi karfin kasa guda.

Shiyasa wannan kasashe suka kawo shawara ga shugaban kasar Nigar akan ayi taro a tattauna akan wannan batu, ya kara da cewa makamai dake shiga Nijar daga libiya ake kawowa, da motocin sata da ma muggan kwayoyi, ya ce dole a dau mataki akai. Sakataren harkokin wajen kasar Sudan Abdulkarim Abdulganiy ya ce maida hankali ga musanyar bayanai itace hanya mafi a'ala wajen cimma burin da aka sa gaba, inda kuma munistan cikin gidan kasar Chadi Ahmad Bashir ya shawarci kasashen hudu akan daukan mahimmam matakan shige da fice, wato karfafa tsaro akan iyakoki da tsananta bincike musamman iyakokin Libiya ta bangaren gabas da kudu maso gabas a sakamakon lura da yanayi da kasar ta Libiya ta haifar a kasashe makwaftan ta yasa taron bayyana shirin danka al'amura a hannun kwararru domin jnin ta bakin su a kan nabubuwan da suke ganin sune mafita, sun bayyana cewa taron ministocin zai bada sanarwar karsehn taro dauke da alkawuran ko wacce daga cikin kasashen hud da suka kira kansu kasashe mafi dandana kudar tabarbarewar al'amuran hukuma a kasar Libya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG