Gamsuwa da yadda kungiyar dalibai ta kasa ta soma biyayya da wasu sharuda da gwamnatin Niger ta gindaya a matsayin na share fagen shiga tattaunawa a tsakanin ta da dalibai ya sa hukumomin ilimi yanke shawarar sake bude wuraren kwanan dalibai inji ministan Ilimi Yahuza Salisu, inda yace wajibi ne gwamnati ta bude wuraren kwana da wuraren abinci domin su ci gaba da karatun su tunda sun janye yajin da sukeyi.
Shuwagabannin kungiyar dalibai sun yaba da wannan yunkuri da suke kallo a matsayin matakin kubutar da sha'anin ilimi daga dabaibayin da yake fama dashi.
Tsalha Kaila wani kusa a kungiyar dalibai ya ce za ayi amfani da wannan yajin aiki domin a duba wadansu abubuwa wadanda dalibai ke bukata lallai, gwamnatin kuma tayi alkawarin daukar matakai domin kawo karshen matsalolin da ke hana ruwa gudu a jami'oin kasar ta yadda baza a sake samun tarnaki ba a fannin ilimi.
Facebook Forum