Hukumomi a Nijer sun ce sai magani na dauke da takarda dake tabbatar da igancinsa da kuma kasar da aka shigo da shi, sa’annan a amince da maganin kuma a bada izinin sayar da shi a shagunan sayar da magunguna na cikin kasar.
A zantawarsu da wakilin sashen Hausa a birnin Yamai Sule Mumuni Barma, ministan kiwon lafiyar Dr Ilyasu Idi Mainasara yace gwamnati ta tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama da laifin shigo da maganin jabu.
Ministan kiwon lafiya ya kara da cewar, gwamnati ta dauki ma’aikatan sa ido akan magungunan jabu da ake shigowa dasu a cikin kasar da dama da zasu rika bincike shagunan magani. Yace gwamnati da dakatar da bada takardan lasisi na shigowa da magani.
Minista Ilyasu Idi Mainasar ya yi karin haske a kan matakai da hukumomin kasar ke dauka na hana shiga da magungunan jabu a cikin kasar a hirarsu da wakilin sashen Hausa.
Facebook Forum