Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Agaji Ta Yi Gargadin Fuskantar Karancin Abinci a Sudan


Sudan
Sudan

Kungiyar agaji ta Mercy Corps ta ce fada da ake ci gaba da yi a Sudan na iya janyo mummunar matsalar abinci. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen gabashin Afirka suka ce suna shirin ganawa da masu ruwa da tsaki a fadan Sudan don samar da masalaha.

Idan ba a daina fada a Sudan ba za a iya fuskantar mummunar matsalar abinci, in ji Freydoun Borhani, shugaban tawagar kungiyar Mercy Corps a jihar Gedaref, da ke kan iyakar Sudan da Habasha, arewa maso gabashin Sudan.

Ya ce “a yanzu haka, lokacin damina a jihar Gedaref alal missali, dole ne mutane su sayi iri don yin shuka, farashin iri ya hauhawa sosai. Hakan yana haifar da matsala ga manomi.”

Amma ba wannan ne kawai kalubalen da manoma ke fuskanta ba, in ji Borhani.

Mercy Corps ta yi shirin raba iri ga manoma kusan 2,100 a jihohi uku da suka hada da Gedaref da Nyala da kuma Kordofan, amma saboda dalilai na tsaro ta raba irin ga manoma 700 a Gedaref.

Sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta sa'o'i 24 da Amurka da Saudiyya suka cimma ta kare da sanyin safiyar Lahadi, kuma yakin ba ya nuna alamun kawo karshe a wasu sassan babban birnin Khartoum da sauran wurare.

A ranar Talata mai zuwa, shugaban kasar Kenya William Ruto ya ce shi da wasu shugabannin kasashen gabashin Afirka na shirin ganawa da bangarorin dake fada da juna a Sudan, domin tattauna hanyoyin kawo karshen yakin. Sanarwar ta biyo bayan taron shugabannin kasashe da gwamnatocin da kungiyar IGAD ta Gabashin Afirka ta kira a Djibouti a farkon makon nan.

XS
SM
MD
LG