washington dc —
A yau talata Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojin Najeriya.
A watan Oktoban daya gabata Shugaba Bola Tinubu ya nada Oluyede a mataki na riko sakamakon rashin lafiyar tsohon babban hafsan sojin Taoreed Lagbaja.
Daga bisani Lagbaja ya mutu a ranar 5 ga watan Nuwambar da muke ciki kuma tuni aka birne shi.
Dandalin Mu Tattauna