Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Muhawara Game Da Batun Janye Takara Da Wasu Ministoci Su Ka Yi


majalisar dokoki ((Facebook/Femi Adesina))
majalisar dokoki ((Facebook/Femi Adesina))

Masana dokokin kasa da masu sharhi akan harkokin siyasar Najeriya sun fara mahawara game da  batun janye takara da wasu ministocin shugaba Muhammadu Buhari suka yi da kuma sahihancin komawa su ci gaba da rike mukaman su.

Duk kuwa da cewa an hangi fuskokin su a wurin liyafar bankwana da shugaba Buharin ya shiryawa ministocin da suke neman takara a matakai daban daban.

Kwana guda bayan umarnin sauka daga mukamai ga wadanda ke da muradin tsayawa zabe a cikin ministocin nasa ranar larabar da ta gabata, shugaba Buhari ya kuma shirya musu liyafar bakwana a fadarsa dake Abuja.

Ko da yake ministan shari’a Abubakar Malami da takwaran na kwadago Chris Ngige sun halarci liyafar, wadda hakan ke nuna cewa, sun shiga jerin masu tsayawa zabe, amma daga bisani ministocin biyu sun sanar da jayewar daga neman takara.

Wannan mataki ya haifar da ayoyin tambaya game da makomar mukaman su, inda ‘yan Najeriya, musamman masana dokokin kasa da masharhanta a fagen demokaradiyya ke tafka mahawara.

Femi Falana mai lambar aikin lauya ta SAN na mai ra’ayin cewa, tunda ministocin biyu sun fita daga ofis tilas ne sai shugaba Buhari ya sake mika sunayen su ga majalisar dattawa domin tantancewa, kafin su iya komawa bakin aiki, yana mai kafa hujja da sashi na 306 na kundin mulkin kasa.

Hakan dai na kara nanata muhimmancin bukatar fadar shugaban kasa ta fayyace al’amura domin ‘yan kasa su sami waraka.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG