Majalisar dattawan Najeriya, ta fara mahawara kan kasafin kudin bana Naira Tiriliyon 6.8, bayan wasikan gyaran kasafin da shugaba Buhari ya aikewa da majalisar biyo bayan labarin da ake cewa kasafin asali ya bace daga zauren majalisar.
‘Yan jami’yyar adawa ta PDP,a majalisar sun dauki salon sukar tsarin kasafin da cewa ba zai samu nasara ba har dai ba’a sauya shi ba, dan an dora wani sa shinsa da zai fito daga mai bisa dala 38,kan gangar mai amma yanzu gangar ta sauko zuwa dala 27.
‘Yan APC, a nasu bangaren na nuna cewa ba’a taba kasasfin kudi mai ma’ana irin na wannan karon ba, da dagewa cewa aima Gwamnatocin baya basu taba aiwatar da kasafi fiye da kashi 40,cikin 100, ba wannan mahauwara ta mai bazata taimaka ba a cewar masanin tattalin arziki na Kwalejin kimiya da fasaha ta Kaduna El-Haroun Muhammad, wanda yake gani yayin dogaro da mai ya kusa wucewa.
Yana mai cewa nahiyar Afirka, masamman kuma Najeriya,Allah ya bata hanyoyin bunkasa tattalin arziki bila addadin gudaya kawai idan aka rike zai bada fiye da abunda tarayyar Turai ke samu a shekara.