Yace yana cikin jerin gwanon motocin sa na shugaban rundunar sojan Najeriya, kuma ya baro Dutse ne da safiyar ranar domin halartan bikin yaye daliban soja rukuni na 73, inda sun shigo Zaria sai suka samu an tare musu hanya’’.
Wadanan sune kalamam babban hafsan sojan Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Burutai ne ke bada ba’asi a lokacin arangamar su da ‘yan shia a zaria, a gaban kwamitin sauraron bayanai na hukumar kare hakkokin bani Adama na Najeriya.
‘’Yace sunzo nan ne domin mu masu mutunta hakkokin ‘yan adam ne, muka sayar da rayuwar mu saboda kare sauran rayuwar al’umma.Ba yadda za’ayi haka kawaai mu dau makamai mu far ma mutanen da muke kare rayuwar su, kuma ku duba tarihin yakin basasan Najeriya, yadda sojoji suka sayar da rayukan su domin tabbatar da hadin kan Najeriya’’
Janar Buratai yace aikin su kullun shine kare diyauci da yancin ‘yan Najeriya.
Kungiyar dalibai suma sun kai nasu korafin daidai lokacin da sojojin suka zo, abinda yasa dole daliban suka ja da baya domin gudun kar a sake samun wani akasin.
Yanzu haka dai an ware ranar laraban nan ta zama ranar kai koken ‘yan shia.
Amma daliban suka yo gaba da nuna cikin wadanda suka rasa rayukan su a Hussainiyar Zaria da gidan Sheik Elzaz-zaki a Gyellesu akwai kimanin dalibai ‘yan shia 30.
Daya daga cikin daliban mai suna Saminu Araze ya shaidawa wakilin sashen Hausa Nasir Adamu El-hikaya cewa kwanan sa ne ke gaba a ranar da aka yi wannan arangamar, wanda ke nuna cewa har yanzu akwai tsama tsakanin su da sojoji.
Ga Nasir Adamu El-Hikaya da Karin bayani