A cikin hirarshi da Sashen Hausa jim kadan bayan da aka rantsar da shi, Sunday Dare ya bayyana godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bashi damar bada gudummuwa a shirin gwamnatin na daga matsayin kasar.
Yace akwai aiki tukuru gabansu na inganta rayuwar matasa wadanda ya bayyana a matsayin shugabannin gobe. Yace zasu sake tunanin matasa da kuma alkiblar su da nufin ganin sun fahimci irin rawar da zasu iya takawa ga ci gaban kasa da kuma gudummuwar da zasu bada a yunkurin gwamnatin na inganta rayuwarsu da kuma damawa da su.
Ya bayyana cewa zasu bi tsarin aiki na kofa bude da zai bada damar tuntuba da sauraron shawarwari idan ta kama, duk da cewa, wadansu lokuta ba lallai matakan da za a dauka su yiwa wadansu dadi ba kasancewa bukatu da ra'ayoyin jama'a sukan banbanta, amma a karshe duka, manufar ita ce, ci ganin an bukasa harkokin wasanni da kuma rayuwar matasa.
Kafin zama shugaban Sashen Hausa, Sunday Dare ya yi aiki da jaridu da dama da suka hada da mujjallar "The News" da ta yi fice a zamanin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida da aka rika gallazawa 'yan jarida.
Tsohon shugaban Sashen Hausan Hausan wanda ya sami digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria a fannin ilimin hulda da kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a Jami'ar Jos a fannin huldar diplomasiya, ya kuma je karo ilimi a fitattun makarantun Amurka da Ingila Harvard da Oxford.
Sunday Dare wanda ya kware a rubuce rubuce da gabatar da kasidu, da suka hada da littafin da ya rubuta da ya shafi aikin jarida "Guerrilla Journalism Speeches from Underground", daya daga cikin littatafan aikin jarida dake dakin karatun jami'ar Harvard.
Kafin bashi mukamin Minista, Sunday Dare Kwamishina ne a hukumar sadarwa ta kasa.
Facebook Forum