Wannan gargadin na zuwa ne bayan da wasu ‘yan kasar suka fara korafi a kan yadda aka fara fuskantar karin kudin motocin haya a washegarin karin kudin man dizel din da aka fuskanta a farkon watan nan na Agusta sanadiyar abin da aka kira mamayar Rasha a Ukraine.
Ta hanyar wata sanarwar da ofishin ministan sufuri ya fitar ne hukumomin Nijer suka ja hankalin drebobin motocin haya wadanda suka hada da tasi da faba faba dangane da abin da aka kira rashin dacewar karin kudin irin wadanan motoci da galibinsu ke amfani da man fetur wato ‘essence’.
A hirar shi da Muryar Amurka, Malan Sama’ila Dan Issa darektan kula da harakokin zurga zurgar motoci a ofishin ministan sufuri ya bayyana damuwa a kan yanda masu motocin ke wuce gona da iri a kan karin kudin mota.
Wannan kashedi na zuwa a wani lokacin da kamfanonin jigilar motocin bus bus wato ‘gares modernes’ a na su bangare suka yi karin kashi 10 daga cikin 100 na kudin motar da aka saba biya daga wannan gari zuwa wancan kafin gwamnatin Nijer ta kara kudin man diezel.
Sai dai gamayyar kungiyoyin drebobin motocin haya ta UTTAN na ganin alamun rashin adalci a yunkurin na mahukunta a bisa la’akari da wasu hujjoji. Sakataren kungiyar drebobi ta SYNCOTAXI Gamatche Mahamadou shine kakakin wannan hadaka wanda kuma yace rashin adalci ne a ba wasu daman kara kudin mota amma a hana wasu yin haka.
Bayanai sun yi nuni da cewa tuni wannan mataki na hukumomin sufuri ya rutsa da wasu drebobin motocin haya da ake zargi da karin kudin zurga zurga a tsakanin anguwannin birnin Yamai a wunin ranar Talata 16 ga watan Agusta inda aka tsare su a makarantar horon ‘yan sanda.
Ga dai rahoton Souley Moumouni Barma daga birnin yamai: