Wakilin hukumar Majalisar Dinkin Duniya Dakta Eugene Kongnyuy, ya bayyana hakan ne a yayin da hukumar ke yi wa wasu mata masu lalurar ta yoyon fitsari aiki a garin Maiduguri.
Ya ce a kasashen da suka ci gaba, ba a samun wannan lalurar don tuni aka kawar da ita, amma a Najeriya ta yi tsamari inda mata kusan dubu 150 ke fama da ita. Wannan ya jefa mata da dama a cikin rayuwar kunci a yayin da akasarinsu ke fuskantar tsangwama
Yoyon fitsari babbar matsala ce a Najeriya musamman a jihar Borno, a cewar wakilin. Kodayake babu wani takamaiman alkalumma a jihar da za a iya dogara da su, amma saboda ana samun yawan mace-mace a wajen haihuwa kuma inda akwai hakan to dole ne a samu matsalar yoyon fitsari.
Masana sun ce yawanci lalurar na faruwa ne sakamakon auren wuri inda kugun mace bai yi kwari ba ko kuma nakuda mai tsawon lokaci.
Wata mai fama da lalurar ta ce kamu ne bayan haihuwarta ta farko inda ta kwashe kwanaki uku a asibiti ta na nakuda daga bisani likitoci suka yi kokari ciro yaron da karfi, amma wajen jawo shi aka ji mata rauni.
Saurari rohoton
Facebook Forum