Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magatakardan Ofishin Ministan Cikin Gida Ya Ziyarci Tubabbun ‘Yan Boko Haram A Diffa


Magatakardan ofishin ministan cikin gida Malam Idir Adamu, ya kai ziyara a wurin da ake killace da wasu ‘ya’yan kungiyar boko haram da suka mika wuya ga hukumomin jihar Diffa, ta jamhuriyar Nijer.

Babban makasudin wannan ziyara dai shine domin ya ganewa idanunsa irin halin da tsofaffin mayakan ‘yan boko haram din ke ciki tare da tattaunawa da su akan inda aka kwana wajan yunkurin mayar da su cikin al’umma da sama masu abubuwan yi.

Da yake jawabi, magatakardan ofishin ministan ya bayyana cewa dukkan ‘yan kungiyar da suka mika kawunansu, sun bayyana masa cewa sun shiga kungiyar ne a sakamakon alkawarta masu abubuwa masu yawa da aka yi, inda ya kara da cewa abin takaici ne kwarai.

Ya kuma kara da cewa, yana jan hankalin sauran da ke cikin kungiyar da su hankalta domin gujewa aikata abubuwan da zai cutar da ‘yan uwansu da kuma al’umma baki daya.

Malam Idir Adamu, ya yi wannan ziyara ne tare da rakiyar gwamnan jihar Diffa, Malam Dandano Muhamman, da shuwagabannin rundunonin tsaro dake jihar Diffa, inda aka killace tubabbun ‘ya’yan kungiyar su dari da talatin, da gwamnatin kasar ke shirye shiryen mayar da su cikin al’umma da sama masu ayyukan yi domin dogaro da kai.

Ga rahoton Harouna Mammane Bako daga Kwanni jamhuriyar Nijer.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:45 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG