Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na'urorin Zamani Sun Hana Yara Karatun Litattafai A Zahiri


An gudanar da bikin ranar kasashen masu amfani da harshen Faransanci, a Jamhuriyar. Niger na daya daga cikin kasashen dake amfani da wannan harshen na Faransanci, shi ne kuma daliban kasar, ke amfani dashi a makarantu.

Gida raya al’adu na kasar Faransa da Nijar, watau, CCFN dake Damgaram na taka rawar gani irin litattafen da ta tanada domin masu karance karance da bincike a kowane mataki.

Daraktan gidan raya al’adu na Faransa da Nijar, Bawa Sule Kaomi, yace wannan bikin shugaba Jori Hamani da shugaban Faransa na wancan lokacin ne suka assasa.

Gidan raya al’adun ya fuskanci wasu matsaloli a baya in ji Daraktan inda yace litattafai kusan dubu ashirin suka kone, amma ya kara da cewa an samu an maida wasu daga cikin littafen amma wasu kuwa amma daina wallafasu.

Shugaban kungiyar Malamai masu koyar da Faransanci Mammam Waje yace babban kalubale yanzu shi yaran yanzu suna koma baya wajen karance karance.

Ya kara da cewa na'urori zamani kamar su kwamfuta sun daukewa yara hankali domin sun fi son karanta abinda zasu karanta akan kwamfuta maimakon karanta litafi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG