A wani taron koli na musamman da aka gudanar a Nairobi kan ‘yan gudun hijira na Somaliya, shugaban kasar Somaliya Mohammed Abdullahi Mohamed da ake kira Farmajo, ya yi kira ga shugabannin hukumar kula da bunkasa harkokin kasashen su taimakawa kasarsa samun hanyar shawo kan matsalar ‘yan gudun hijira.
Bisa ga cewar Majalisar Dinkin Duniya, sama da Somaliyawa miliyan biyu suka rasa matsugunansu a yakin basasan da ya shiga shekara ta ishirin da shida yanzu.
Yace Somaliyawa bisa radin kansu, sunyi ta komawa gida cikin shekaru da suka shige, ganin lamura a kasarsu suna ingantuwa sannu a hankali, sai dai shugaban kasar yace har yanzu akwai kalubalai.
Yace fari da ake fama dashi da kuma yiwuwar fuskantar yunwa wata kalubala ce ga wadanda suke komawa bisa radin kansu. Ya gayawa taron kolin cewa, bai kamata a bari kasar Somaliya ta sake fadawa yanayin yunwa ba.
Facebook Forum