Shugaban kungiyar na kasa Aliyu Jahundi yace sun nuna goyon bayansu ne ga bangaren Ingilishi a wani taronsu da suka yi a birnin Yaounde.
Su dai al'ummar bangaren Ingilishin sun bukaci gwamnatin kasar ta Kamaru ta canza salon mulkinta daga gwamnatin jamhuriya zuwa gwamnatin tarayya.
'Ya'yan kungiyar SDF sun ce dole ne gwamnati ta yadda da muradun bangaren Ingilishin kana da babbar murya suka kira gwamnatin kasar da ta sako malaman makarantu da lauyoyi har ma da fararen hula wadanda aka kama yayinda suke zanga zanga a birnin Baminda.
Mai magana da yawun kungiyar Malam Bala Maikwari ya bayyana dalilin da suka ce a sako wadanda ake tsare dasu. Injishi an kamasu ne ba kan ka'ida ba. Kazalika duk wanda yake neman 'yancin kansa ba za'a kamashi kaman dan ta'ada ba,
Jibrilla Jibo wanda shi yana bangaren gwamnati ne yace wajibi ne a kama mutanen a kuma yi masu hukumci. Yace Kamaru daya ce kuma ba'a son zalunci.
'Yan adawan sun ce tun shekarar 1977 suke fafutikar neman a canza gwamnati daga jamhuriya zuwa ta gwamnatin tarayya.
Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.
Facebook Forum