Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Facebook Ya Taimaka Wajen Yaki Da Safarar Mutane A Afrika


Hukumar shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya, tayi kira ga kamfanin Facebook, ya kokarta wajen dakile shafufuka da mutane kanyi amfani da su wajen tallata wasu ayyuka da suke samar wa matasa a kasashen Turai, a duk lokacin da suka fitar da su kasashen waje.

Hukumar ta kara da cewar, mafi akasarin mutane da ke safarar mutane daga kasashen Afrika zuwa kasashen Turai, suna kwadaita ma matasa wasu abubuwan jin dadin rayuwa, wanda suke tabbatar musu da cewar idan sun isa can turai zasu basu.

Da yawa sukan dauki matasan su tafi da su ne don su sayar da su, ko a saka su cikin aikin bauta, ko kuma aikin karuwanci. Su kan yi musu alkawura na cewar zasu samar musu aikin yi.

Mai magana da yawun kungiyar Mr. Leonard Doyle, ya ce ana amfani da shafin na Facebook wajen tallata wadannan miyagun dabi’un, wanda daga bisani akan dauki hotunan matasa da irin yadda ake azabtar da su, ana aika ma dangin su a Afrika.

Wanda hakan yake sa dangin nasu zasu fitar da kudade da zasu aika don ceto rayukan ‘yan uwansu. Alkalumma sun tabbatar da cewar, mutane dubbai ne suka mutu a kokarin tsallake teku don zuwa Turai.

Tun daga shekarar 2014 ake mutuwa, kimanin mutane 3,091 suka mutu a wannan shekarar cikin teku, wasu kuwa bayan sun bar kasar Libiya suka mutu. A wannan shekarar kawai akwai mutane sama da 165,000 da suka samu nasarar shiga Turai.

A irin yanayi da kasashen Turai suke ciki yanzu na siyasa, babu dalilin da zai sa mutun ya bar kasar shi, da yake da ‘yanci don zuwa wata kasa bauta, domin kuwa wadannan mutane dake tallata irin wadannan aiyukan a kasashen Turai ba gaskiya suke gaya ma mutane ba.

Don haka matasa suyi taka tsan-tsan wajen barin kasashen su da niyyar zuwa kasashen Turai da sunan neman arziki, domin kuwa su kansu kasashen suna cikin mawuyacin yanayi a yanzu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG