Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isira'ila Ba Ta Kunyar Far Ma Kananan Yara - Ayatollah Ali Khamenei


Babban shugaban Addinin kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei
Babban shugaban Addinin kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei

Shugaban addinin Iran, Ayotollah Ali Khamenei, jiya Asabar ya ce Isira’ila na aikata “babban laifi na marasa kunya” ga yara kanana, amma ba ga mayaka ba.

Kalaman na sa na zuwa ne kwana guda, bayan da wani harin da Isira’ila ta kai ta sama kan Beirut, babban birnin Lebanon, ya halaka mutane a kalla 31, ciki har da yara uku da mata 7, a cewar Ma’aikatar Lafiyar Lebanon.

Harin na ranar Jumma’a, wanda a cewar wasu majiyoyi ya auna wani gini da ke kusa da wata makarantar nursery, shi ne mafi kisa a tsawon shekara guda, a tashin hankalin Isira’ila da mayakan Hezbolla na Lebanon, masu samun goyon bayan Iran.

Wannan hari ya biyo bayan wasu hare haren da aka kwashe kwanaki biyu ana kaiwa, inda aka sa na’urorin sadarwa na pagers da kuma na oba oba, da ‘yan Hezbollah ke amfani da su, su ka yi ta bindiga. Lebanon dai ta dora laifin wannan harin kan Isira’ila, wadda ita kuma ta ki tabbatarwa ko karyatawa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG