Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mabiya Addinin Kirista Sun Yi Bikin Kirsimeti Tare Da Gudanar Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya


Bikin Kirsimeti
Bikin Kirsimeti

Mabiya addinin Kirista sun yi bikin Kirsimeti tare da gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da samun shugabanni nagari a zabukan dake zuwa a shekarar badi.

Bikin na Kirsimeti ana gudanarwa ne a kowace ranar ishirin da biyar ga watan Disamban kowace shekara don tunawa da haihuwar Yesu Almasihu.

Madam Afiniki Barem Bako dake bikin na Kirsimeti tace bayan tayi sujjada zata ziyarci ‘yan’uwa don basu kyaututtuka da kuma fadakar da mata muhimmancin karbar katin zabe,

Shi ma Mr Emini Blessing ya ce sun gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a kasa.

A hudubar da ya gudanar a Majami’ar Cibiyar Tauhidi ta ECWA wato ECWA Seminary Church Jos, Pastor Yakubu Yusuf Jakheng ya ce akwai begen samun canji mai inganci a Najeriya da Duniya baki daya.

A halin da ake ciki dai, mabiyan na Almasihu na ci gaba da bukukuwa wanda a yau Litinin za a ci gaba da ziyarar bada kyaututtuka wa ‘yan’uwa da abokan arziki, da ake kira Boxing Day.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG