ABUJA, NIGERIA - Masana sun alakanta haka da tsadar dala akan Naira da kuma karancin man fetur da ya hana wasu tafiye-tafiye kamar yadda aka saba a lokutan bukukuwan shekarun baya.
Masu bibiyan al’amura na cewa bikin na bana ya zo cikin wani yanayi a Najeriya sakamakon hauhawar farashi a canjin kudin dala akan Naira da karancin man fetur wadanda suka shafi rayuwar al’umma ta yau da kullum.
Tun watan Nuwanban da ya gabata ne hukumar kididdiga ta Najeriya wato NBS ta fitar da rahoton da ya yi nuni kan karin da aka samu a hauhawar farashin kayaki da kaso 21 da digo 47 cikin 100 adadin da ya kasance mafi yawa cikin shekaru 17 da suka wuce, kamar yadda Masanin tattalin arziki Dakta Isa Abdullahi ya bayyana mana.
A duk shekara akan samu kari a farashin kayakin abinci da kusan kaso 150 a lokutan bukukuwan karshen shekara.
Masana sun ce kari da ake gani a farashi kowace litar man fetur da na dezel baya rasa nasaba da karin bukatun tafiye-tafiye da ‘yan kasar ke yi sakamakon gabatowar bukukuwan Kirsimeti domin a koma garurruwan asali don gudanar da shagulgula da ‘yan uwa da abokan arziki.
Da muka ziyarci kasuwannin Utako, Wuse da Garki duk a birnin Abuja, wasu ‘yan kasar sun bayyana mana ra’ayoyinsu a game da farashin wasu kayakin masarufi a daidai wannan lokaci.
Tun daga shekarar 2016 ne Najeriya ke fama da hauhawar farashi mai lamba biyu, lamarin da ya haifar da karin farashin kayaki da ayyuka cikin sauri a bana.
Kazalika, masana tattalin arziki sun ce matakin da gwamnatin kasar ta dauka na canja launin takardar kudinta da tsarin takaita adadin kudin da ‘yan kasar zasu iya cirewa a cikin asusunsu na bankuna a kullum na daga cikin dalilan da suka haifar da yanayin da al’umma suka tsinci kansu ciki.
Saurari cikakken rahoto daga Shamsiyya Hamza Ibrahim: