ENUGU, NIGERIA - Dillalan dai sun yi ittifaki kan cewa cinikin Kirsimetin bana ya yi karanci matuka idan aka kwatanta da na lokutan baya.
Shugaban kungiyar dillalan kifi a kasuwar Akwata da ke birnin Inugu, Alhaji Kaka Modu Waziri ya koka cewa suna tabka asara sosai saboda akwai kifi jibge amma babu masu saye.
Ya ce, “cinikin dai babu sosai. Ba kamar irin na shekarun baya ba saboda bana ga kaya amma babu masu saye sosai. Mu da kanmu asara muke tabkawa. Su ma masu saye yadda muke kuka haka ma suke kuka. Wallahi akwai kifi, tsadar rayuwa ce, kawai tsadar mai ce. Yanzu kudin mota daga Jihar Adamawa zuwa nan nera miliyan daya da dubu dari shida muke biya.”
Haka zalika shi ma Malam Yusha’u Mati yana gannin tsadar rayuwa ce ta janyo karancin cinikin.
Ya ce “Ciniki ya yi baya ba kamar Kirsimetin bara ba. Yanzu wannan satin shi ne karshen kasuwar Kirsimeti a wurinmu, amma har yanzu ga shi nan muna fama da kaya saboda tsadar rayuwa ta yi yawa. Kudin motan da muke biya da daga Arewa zuwa Kudu an kara an ninka. Toh yanzu kayan da muke kawowa sai dai a taya mana kasa da yadda muka sayo shi.”
A cewar Mista Alexander Okenyi, “wannan shekarar kwana uku kafin Kirsimeti babu ciniki. Mu dillalai masu sayar da kifi mun fi masu saya yawa. Wannan shekarar babu ciniki kwatakwata. Gaskiya abin ya dame mu.”
Shi kuwa Alhaji Mamuri Gana ya lura cewa sake fasalin kudin nera wanda gwamnatin tarayya ta yi ne ya ke shafar ciniki a daidai wannan lokacin.
Ya ce, “yanayin canjin kudin nan ne ya janyo wannan matsalar saboda sam-sam babu kudi a hannun mutane. Wasu suna tsammanin cewa sabon kudin zai shigo kasuwa a wannan watan, amma har yanzu bai shigo ba. Yanzu dole gwamnati ta kara wa’adin da ta bayar saboda baza a samu kudin ba idan bata kara wa’adi ba.”
Saurari cikakken rahoto daga Alphonsus Okoroigwe: