Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afrika Na Da Gudummuwar Da Zata Bayar Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya - Amurka


Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris a Ghana
Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris a Ghana

Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta bayyana cewa shugabannin nahiyar Afrika na da gudunmuwar da zasu bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasashen duniya.

Kamala Harris ta bayyana hakan ne a lokacin da ta gana da matasa a Accra babban birnin Ghana, inda ta jaddada muhimmanci nahiyar Afrika ga duniya musamman Amurka.

Mataimakiyar Shugaban kasar Amurka, Kamala Harris a taro da matasa lokacin ziyarar aiki kasar Ghana.
Mataimakiyar Shugaban kasar Amurka, Kamala Harris a taro da matasa lokacin ziyarar aiki kasar Ghana.

"Kafin shekarar 2050 mutum daya cikin hudu a fadin duniya zai kasance daga nahiyar Afrika. Wannan na nuni da cewa duk wani abin da ke faruwa a wannan nahiyar zai yi tasiri akan duniya sosai,” a cewar Harris.

Ta kara da cewa “ganin ku a nan ya sanya ni farin ciki sosai akan makomarmu. Kamar yadda shugaban Amurka Joe Biden ya fada a taron Amurka da nahiyar a bara, cewa mu duka muna tare da nahiyar Afrika saboda nahiyar na da gudummuwa mai muhimmancin gaske da zata bayar wajen tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, kamar abubuwan da ke da muhimmanci ga al’umar Amurka da suka hada da samar da abinci, matsalar sauyin yanayi, da kiwon lafiya."

Daya daga cikin masharhanta kan harkar tsaro da diflomasiyya a Ghana Adib Sani, wanda shi ma ya halarci taron ya yi na'am da tsokacin da Kamala Harris ta gabatar kan gudummuwar da nahiyar Afrika zata bayar wajen zaman lafiya da tsaron duniya, inda ya ce Amurka na harkar kasuwanci da Afrika bayan tallafin da take ba kasashen nahiyar, kuma matsalar tsaro a kasashen Mali da Burkina Faso ta zamo wani abin damuwa sosai ga kasar Amurka, a saboda haka Amurka ta yi alkawalin bai wa wasu kasashen yamacin Afrika dala miliyan 100 domin karfafa tsaro a yankin da ke da iyaka da teku.

Ziyarar Kamala Harris Ghana
Ziyarar Kamala Harris Ghana

Ya kuma kara da cewa yanzu batun tsaro ya zamo wani lamari da duniya ta damu da shi kuma abinda ke faruwa a Burkina Faso zai iya faruwa a wata kasa.

Sai dai ba batun tsaro kadai mataimakiyar shugaban Amurka ta yi magana akansa ba, har ma da batun bai wa mata dama da ma bunkasa harkar fasahar zamani.

Saurari cikakken rahoton Hamza Adam:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

XS
SM
MD
LG