Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar Tsaron Amurka Ta Ce Syria Bata Shirin Kai Wani Hari Da Makami Mai Guba


Dana White mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaron Amurka tare da Janar Kenneth McKenzie na sojojin kuntunbala ko Marines
Dana White mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaron Amurka tare da Janar Kenneth McKenzie na sojojin kuntunbala ko Marines

A cewar ma'aikatar tsaron Amurka, sanadiyar harin taron dangi da suka kai kan Syria, gwamnatin kasar bata shirin sake kai wani hari da makami mai guba kan mutanen kasarta amma dai Amurka da kawayenta suna cikin shirin ko ta kwana

Maaikatar tsaron Amurka tace ga bisa dukkan alamu ba wani sabon yunkuri daga gwamnatin Syria cewa zata sake kai wani sabon harin makami mai guba, hakan koba zai rasa nasaba da harin hadin gwuiwa na ranar Asabar din da Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai ma kasar ba.

Sai dai mahukuntar Amurka sunce Amurka da sauran kawayenta suna nan cikin shirin ko ta kwana.

Mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron na Amurka Dana White ta fadawa manema labarai jiya Alhamis cewa Shugaban Syria Bashar Al-Assad tilas ya kwana da sanin cewa duniya ba zata amince da yin anfani da makami mai guba ba akan ko wane irin dalili.

Harin dai da Amurka ta jagoranta ya zo ne a matsayin martini ne a harin makami mai guba da ake tuhumar ya kashe mutane 40 fararen huka a Douma ranar 17 ga watan Afirilu.

Amurka tace Syria ca ke da laifin kai wannan harin.

Sai dai Syrian da kawarta Rasha sun musunta anfani da duk wani makami mai kama da wanda ake tuhuma Syria tayi anfani dashi.

White ta ce biyo bayan harin da aka kaiwa Syria sai Rasha ta fara kamfen din ruda mutane domin ta shuka kwokwanto da rudani domin boye wannan mummunar aikin da ake tuhumar Syrian da aikatawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG